180313-Jakadan-Najeriya-a-kasar-Sin-ya-yi-tsokaci-kan-muhimman-taruka-biyu-na-kasar-Sin.m4a
|
Ga masu bibiyar al'amurran dake wakana a siyasar duniya, a ranar 3 ga watan Maris ne aka bude taron majalisar bada shawara kan harkokin siyasar kasar Sin wato CPPCC, kana a ranar 5 ga wata aka bude taron majalisar wakilan jama'ar kasar ta Sin wato NPC, sakamakon wadannan muhimman taruka biyu, shirin Sin ta Afrika ya tattauna da jakadan Najeriya a kasar Sin Ambasada Baba Ahmad Jidda, inda ya bayyana yadda ya fahimci wadannan muhimman tarukan biyu da kuma alfanin da suke da shi ga ci gaban kasar Sin, kana ya yi tsokaci game da sauran batutuwa da suka shafi dangantaka tsakanin Sin da Afrika. Ga cikakkiyar zantawarmu da Ambasa Ahmad Jidda.