in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan tarukan kasar Sin NPC da CPPCC na shekarar 2018
2018-03-08 07:40:43 cri

Daga rakanun 3 zuwa 5 ga watan Maris na shekarar 2018 ne aka fara taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC a takaice da kuma majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin NPC na shekara-shekara a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin inda majalisun za su tattauna batutuwan da suka shafi makomar kasar Sin baki daya.

Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, majalisa ce da ta kunshi mambobi daga sassa daban-daban na kasar da suka hada da jam'iyyun siyasa, kungiyoyi da wakilai masu zaman kansu.

Kuma bisa al'ada, jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin ce ke da wakilai mafi rinjaye a majalisar, inda take da kashi 1 bisa 3 na daukacin mambobin majalisar. Sauran mambobin majalisar sun fito ne daga jam'iyyun da ke kawance da jam'iyyar kwaminis mai mulki da sauran wakilai masu zaman kansu wadanda ba sa cikin kowace jami'yya.

Ita kuma majalisar wakilan jama'a wato NPC a takaice majalisa ce da ake zaben wakilanta daga mazabun gundumomin kasar, yankuna masu cin gashin kansu, birane karkashin kulawar gwamnatin tsakiya, rundunar sojojin kasar da sauransu.

Aikin majalisar wakilan sun hada da gyaran kundin tsarin mulkin kasa da sanya ido wajen ganin an aiwatar da tanade-tanaden da ke kunshe cikin kundin tsarin mulkin kasar, kafa dokoki da suka shafi manyan laifuffuka, harkokin jama'a, hukumomi da ma'aikatun gwamnati da sauran batutuwan da ke shafar rayuwar Sinawa.

Har ila yau, majalisar wakilan ce take zabe da kuma nada wadanda za su jagoranci hukumomin gwamnati da yanke hukunci game da manyan batutuwan da suka shafi kasa baki daya.

Masana na bayyana cewa, kamar yadda aka saba a tarukan na bana ma, ana sa ran za a tattauna muhimman batutuwa kamar, shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki, da matakan inganta rayuwar al'umma da, manufofin diflomasiyar kasar Sin, da sauran muhimman batutuwa da suka shafi kasar Sin da matakan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki. (Ahmad, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China