A cikin rahoton aikin gwamnatin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar a wajen taron shekara-shekara na majalisar NPC wanda aka bude a yau Litinin, an nuna cewa, a bana, kasar Sin za ta fadada harkokin shigo da kayayyaki daga ketare, da kara samar da sauki da tabbatar da samun 'yanci a harkokin cinikayya da zuba jari.
Rahoton ya kuma jaddada cewa, Sin ta bada shawarar a rika daidaita sabanin cinikayya ta hanyar yin shawarwari cikin adalci da nuna kin amincewa da matakan cinikayya masu tsauri da kuma tsayawa kan kare halattaccen hakki. (Murtala Zhang)