in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara-shekara na majalisar NPC
2018-03-05 09:10:26 cri

Da safiyar yau Litinin, a Beijing, fadar mulkin kasar Sin, aka kaddamar da zama na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 wato NPC, inda shugaba Xi Jinping da sauran wasu manyan shugabannin jam'iyyu da na kasar Sin suka hallara.

Yayin taron, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da rahoton aiki kan gwamnatin kasa, inda kuma mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar NPC karo na 12, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin, Wang Chen, ya yi bayani kan daftarin shirin yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasa.

Wannan ne karon farko da sabuwar hukumar kolin kasar Sin ta kira taro bayan da aka gudanar da babban taro karo na 19 na wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar a bara.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China