in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe cikakken taro na 3 na kwamitin tsakiya na 19 na JKS
2018-03-01 10:58:50 cri

Jiya Laraba 28 ga watan Fabrairu, aka rufe cikakken taro karo na 3 na kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda aka shafe kwanaki 3 ana gudanarwa a nan birnin Beijing, yayin taron, an dudduba kuma aka zartas da jerin sunayen sabbin shugabannin hukumomin gwamnatin kasar da majalisar bada shawara kan harkokin siyasa da aka gabatar, kana aka zartas da kudurin game da kara zurfafa gyaran fuska ga hukumomin JKS da gwamnatin kasa da shirin dake jibanci gyaran fuskar, kuma babban sakataren JKS Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi a yayin taron.

A cikin rahoton da aka gabatar bayan da aka kammala cikakken taron karo na 3 na kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, an bayyana cewa, an gabatar da wannan jerin sunayen sabbin shugabannin hukumomin gwamnatin kasar da majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ga kungiyar shugabannin taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da kungiyar shugabannin taro na farko na majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ne bayan da hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS ta yi tattaunawa sau da dama da wakilan da suka fito daga fadin kasar, wato suna kumshe da 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da wadan da bana JKS ba, kana an tsai da cewa, za a gabatar da shirin kara zurfafa gyaran fuska ga hukumomin JKS da gwamnatin kasar ga taro na farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 13 bisa ka'ida domin a duduba shi.

Yayin taron, an dauka cewa, hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS tana gudanar da aikinta yadda ya kamata tun bayan da aka kammala cikakken taro na farko na kwamitin tsakiya na JKS na 19, kuma ana ganin cewa, taruka biyu wato taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da taron majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wanda za a gudana bada dadewa ba, zasu taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi kan aikin kafa zaman al'umma mai matsakaiciyar wadata a dukkan fannoni, da aiwatar da tsarin mulkin na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki cikin nasara, a don haka ana iya cewa, suna da babbar ma'ana.

Yayin taron, an yi nuni da cewa, kara zurfafa gyaran fuska ga hukumomin JKS da gwamnatin kasa zai ingiza kyautatuwar tsarin tafiyar da harkokin kasa, haka kuma zai zamanintar da karfin tafiyar da harkokin kasa, game da wannan sabuwar bakata a sabon zamanin da ake ciki, ya zama wajibi JKS ta yi hanzarin kara karfafa karfinta wajen tafiyar da harkokin kasa ta hanyar kara zurfafa gyaran fuska ga hukumominta, don haka ana iya kara fahimtar fifikon tsarin gurguzu na kasar Sin.

Wakilan da suka halarci cikakken taron sun gabatar da cewa, ana gudanar da gyaran fuska ne domin kafa tsarin aikin hukumomin JKS da gwamnatin kasar mai inganci, da tsarin bada jagoranci kan aikin tafiyar da harkokin kasa na JKS mai amfani, da tsarin aikin hukumomin gwamnatin kasa da za a iya amfani dashi bisa ka'ida, da tsarin rundunonin sojoji mai halayyar musamman ta kasar Sin wanda zai yi rinjaye a fadin duniya, da tsarin aikin kungiyoyi masu zaman kansu wanda zai samar da hidima mai inganci ga al'ummun kasar, don haka majalisar wakilan jama'ar kasar, da gwamnatin kasar, da majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar, da hukumomin sanya ido ta kasar, da hukumomin shara'ar kasar, da hukumomin gabatar da kara na kasar, da kungiyoyin masu zaman kansu, da kamfanonin kasar da sauransu zasu gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu yadda ya kamata karkashin jagorancin JKS, haka kuma za a cimma burin tafiyar da harkokin kasa cikin kwanciyar hankali.

Cikakken taron ya kara da cewa, idan ana son cimma burin kara zurfafa gyaran fuskar a kasar Sin, abu mafi muhimmanci shine a nace ga jagorancin JKS daga dukkan fannnoni, tare kuma da ingiza gyaran fuska ga tsarin ladaftarwa da sanya ido na JKS da tsarin sanya ido na gwamnatin kasa.

Ban da haka kuma, an bayyana cewa, kyautata aikin kafa hukumomin gwamnati, da kafa tsarin tattalin arziki na zamani, da kara saukaka ayyukan hukumomin gwamnati, da kyautata aikin sanya ido ga kasuwa, da kyautata tsarin kula da albarkatun halittu da muhallin masu rai da marasa rai, da kyautata tsarin tafiyar da harkokin samar da hidima ga jama'a, zasu taka muhimmiyar rawa wajen kyautata aikin gwamnatin kasar.

Hakazalika, ya kamata a kara maida hankali kan huldar dake tsakanin hukumomin JKS da gwamnati da rundumar sojoji da kungiyoyi masu zaman kansu yayin da ake gudanar da gyaran fuskar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China