180228-Yadda-aka-gudanar-da-bikin-Bazara-a-kasar-Sin.m4a
|
Hukumar jiragen kasa ta kasar Sin ta bayyana cewa, a yayin wannan biki, zirga-zirga ta jiragen kasa ta kai matsayin koli a kasar, yayin da matafiya ke komawa bakin aiki, bayan kammala hutun bikin bazara na mako guda.
Ita ma hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin ta yi hasashen cewa, daga ranar 1 ga watan Fabrairu zuwa 12 ga watan Maris na wannan shekara za a yi zirga-zirga kimanin biliyan 2.98, wato daidai da alkaluman shekarar da ta gabata.
Daruruwan miliyoyin Sinawa ne dai suke komawa garuruwansu domin murnar bikin Bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin tare da iyalansu.
Kamar sauran lokuta, a wannan shekarar ma mahukuntan kasar Sin ta tanadi matakan tsaro a kan hanyoyi da tashoshin mota da jiragen kasa da na sama da wuraren yawon shakatawa don tabbatar da gudanar da bikin lami lafiya.
Haka kuma kamfanonin samar da hidima da sayar da abinci da sauransu sun kara inganta ayyukansu don biyan bukatun jama'a. Baya ga haduwa da iyalai, bikin ya kuma taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin da raya al'adu da sauran fannoni na ci gaban kasar.
Baya ga kasar Sin, an kuma gudanar da bikin a sassan daban-daban na duniya. Bikin na bana dai ya kammala lafiya, sai kuma na badi idan Allah ya kai mu. (Ahmed, Fa'iza, Ibrahim/Sanusi Chen)