Kwanan baya, ni da Kande mun kai ziyara Tabkin Lugu, mai kama lu'u lu'u ne da aka ajiye a tsakanin duwatsu dake kan iyakar lardunan Yunnan da Sichuan na kasar Sin. 'Yan kabilar Mosuo da har yanzu al'ummarta ke martaba mahaifiya matuka suna zaune a wannan wurin mai ni'ima, al'adun gargajiya irin na da da can na 'yan kabilar ya kara zama wani abin al'ajabi kan wannan tsohon yanki, wannan ya sa ake kira wurin "Kasar mata dake gabashin duniya". Tun daga lokacin da har zuwa yanzu, matan dake wannan "kasar" suna daukar nauyin kula da iyalansu ta hanyar hikima da kwazo. A cikin shirinmu na yau, za mu kai muku wani kauye ne mai suna Daluoshui dake dab da tabkin Lugu, don kawo muku labarin wata mace 'yar kabilar Mosuo mai suna Geze Yongdu.
180226-Geze-Yongdu-yar-kabilar-Mosuo-wadda-ta-hada-raya-sanaa-da-kiyaye-aladun-gargajiyar-kabilarsu-Bilkisu.m4a
|