in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana gudanar da aikin gina layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Beijing da Zhangjiakou lami lafiya
2018-02-22 11:05:50 cri

A shekarar 1905, an gina layin dogo tsakanin biranen Beijing da Zhangjiakou wato hedkwatar lardin Hebei na kasar, layin dogon wanda ya kasance na farko a kasar ta Sin, yanzu ana gina layin dogo mai saurin tafiya dake tsakanin wadannan biranen biyu, wanda zai taka muhimmiyar rawa wajen sufuri yayin gasar wasannain Olympics na lokacin hunturu na shekarar 2022.

A filin da ake gudanar da aikin gina layin dogo tsakanin Beijing da Zhangjiakou dake kusa da garin Taizicheng, ma'aikatan suna shan aiki, har basu samu damar hutawa ba yayin bikin bazara, wanda ya kasance gagarumin bikin Sinawa bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, manajan sashen kula da aikin gina layin dogo a gundumar Chongli dake arewa maso yammacin lardin Hebei na kasar na rukunin gina layin dogo na kasar Sin Cheng Duojin ya yi mana bayani cewa, an yi hasashe cewa, za a kammala aikin a wannan wuri kafin lokaci, yana mai cewa, "Kawo yanzu, an riga an kammala aikin da yawansa ya kai kusan kaso 43 bisa dari, an yi hasashe cewa, ya kamata a kammala aikin gina wurin kafin lokaci har da tsawon kwanaki 15."

Layin dogon tsakanin Beijing da Zhangjiakou reshensa a gundumar Chongli yana cikin birnin Zhangjiakou, tsawonsa ya kai kilomita 52, zai hada da layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Beijing da Zhangjiakou, bisa shirin da aka tsara, za a kammala aikin gina shi a shekarar 2019, da haka za a iya tafiya kai tsaye daga Beijing zuwa masaukin 'yan wasannin Olympics a gundumar Chongli yayin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na shekarar 2022.

Domin cimma burin kammala aikin gina layin dogon cikin lokaci, an kuma yi amfani da wasu fasahohin zamani, a don haka ba ma kawai an kara saurin aiki ba ne, har ma an kara kyautata ingancin aikin.

Hakika ana amfani da fasahohin zamani yayin da ake gina layin dogo mai saurin tafiya dake tsakanin Beijing da Zhangjiakou, wato ba a gundumar Chongli ba kawai, misali a fannonin aikin ginawa da samar da na'urorin zamani da kuma samar da hidimomi masu inganci ga fasinjoji ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani da sauransu.

Layin dogo mai saurin tafiya tsakanin Beijing da Zhangjiakou ya fara ne daga tashar saukar jiragen kasa ta arewa ta birnin Beijing, kuma ya isa ne zuwa birnin Zhangjiakou na lardin Hebei na kasar, tsawonsa zai kai kilomita 173, idan ya fara aiki, ana bukatar mintoci 50 kawai daga Beijjing zuwa Zhangjiakou cikin jirgin kasa, amma yanzu ana bukatar awoyi uku da wani abu.

Mataimakin shugaban sashen kula da aikin ginawa na kamfanin gina layin dogo tsakanin Beijing da Zhangjiakou Li Yanbo ya gaya mana cewa, an fara gudanar da aikin gina layin dogo tsakanin Beijing da Zhangjiakou tun daga farkon shekarar 2016, za a kuma kammala aikin ne a shekarar 2019, wato tare da aikin gina layin dogon reshensa a gundumar Chongli, manyan ayyukan da ake gudanarwa sun hada da kadarko guda daya, da tasoshi guda biyu, da kuma hanyoyi cikin duwatsu guda uku, kadarkon shi ne babban kadarko kan madatsar ruwa ta Guanting,tasoshin biyu sun hada da tashar babbar ganuwa ta Badaling da tashar Qinghe, hanyoyin cikin duwatse su ne hanyar Badaling da hanyar Qinghuayuan da kuma hanyar Zhengpantai, a halin da ake ciki yanzu, an riga an kammala aikin ginawa a kadarkon, saura kuma ana gudanar da aikin lami lafiya, Li Yanbo yana mai cewa, "A takaice dai, ana iya cewa, ana gudanar da aikin yadda ya kamata, wato an riga an kashe kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan biliyan 17, adadin da ya kai kaso 40 bisa dari ke nan, an sa ran cewa, za a kammala aikin daga duk fannoni kafin karshen shekarar 2019."

Li Yanbo ya kara da cewa, idan aka kwatanta wannan layin dogon da layukan da aka gina a baya, a bayyane ne an lura cewa, wannan ya fi zama na zamani, ya ce, "Layin dogo tsakanin Beijing da Zhangjiakou da aka gina a shekarar 1905 shi ne layin dogo na farko da aka gina a kasar Sin, yanzu dai ana gudanar da aikin gina layin dogo mai saurin tafiya tsakanin biranen nan biyu, hakan ya alamanta cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin, dalilin da ya sa haka kuwa shi ne domin ana amfani da fasahohin zamani yayin aikin."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China