180306-Hira-da-shugaban-hukumar-kwastam-ta-Najeriya-Hameed-Ali.m4a
|
A kwanakin baya ne aka shirya wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu game da harkar cinikayya ta yanar gizo tsakanin kasashen duniya.
Taron wanda hukumar kwastan ta kasa da kasa tare da hadin gwiwar takwararta ta kasar Sin suka shirya a nan birnin Beijing, ya samu halartar shugabannin hukumomin kwastan daga kasashe daban-daban na duniya da kuma manyan kamfanonin cinikayya ta yanar gizo .
Shugaban hukumar kwastan ta Najeriya Hamid Ibrahim Ali, yana daga cikin mahalarta taron wanda shi ne irin sa na farko da aka shirya a nan birnin Beijing,fadar mulkin kasar Sin.
A cikin shirinmu na Sin da Afirka na wannan mako, abokin aikinmu Ibrahim Yaya ya tattauna da shugaban hukumar kwastan ta Hamid Ibrahim Ali game da muhimmancin wannan taro da kuma yadda kasashe masu tasowa za su amfana da sabon tsarin cinikayya ta yanar gizo.