180221-Shirin-gwamnatin-Sin-na-raya-kauyuka-da-inganta-rayuwar-manoma.m4a
|
Ofishin kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin ne suka fitar da wannan takarda, inda suka bayyana cewa, za su kara mai da hankali kan aikin kyautata yanayin rayuwar manoma dake kauyukan kasar. A 'yan shekarun da suka gabata, duk da cewa an samu wasu sakamakon a wannan fanni, amma har yanzu akwai rashin daidaito yayin da ake kokarin kyautata yanayin kauyuka.
Takardar ta kuma bayyana cewa, idan ana son cimma wannan burin, akwai bukatar a kara mai da hankali kan fannoni uku, abubuwan shara da zai dace da yanayin da kauyukan ke ciki, da ruwa maras tsabta, da tsarin gine-gine.
Kasar Sin tana da fadi, kuma akwai bambanci tsakanin yankuna daban daban, a don haka ya kamata a bullo da shirye-shiryen da za su dace da wurare daban daban da kuma halin da suke ciki. An yi hasashe cewa, nan da shekarar 2020, yanayin wasu kauyuka dake yankunan kasar Sin, misali, yankunan dake gabashi da tsakiya da kuma yammacin kasar za su inganta.
Masu sharhi na cewa, akwai bukatar a kara samar da kudaden gudanar da wannan aiki, musamman ma a kauyukan dake tsakiya da yammacin kasar ta Sin. A karshe takardar ta bayyana cewa, za a karfafawa kamfanonin kasar Sin gwiwa shiga a dama da su a wannan aikin, ta yadda za su taka rawa tare da gwamnati don cimma wannan buri. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)