in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ayyukan diflomasiyar kasar Sin a shekarar 2018
2018-02-22 15:42:22 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana a kwanakin baya cewa, a shekarar 2018 kasar Sin za ta hada kai da sauran kasashe don ganin an tabbatar da zaman lafiya a duniya, tare da bullo da sabbin dabarun hadin gwiwa da jagorantar al'amuran duniya ta yadda za su kai ga inganta rayuwar al'umma da ci gaban tattalin arziki a ko'ina.

Haka kuma a wannan shekara ce kasar Sin ke shirin karbar bakuncin taron dandalin hadin gwiwar Shanghai (SCO), taron kolin Sin da Afirka (FOCAC), bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su na kasa da kasa da sauransu. Wadannan a cewar Wang Yi, wani sabon babi ne na kawancen moriyar juna da sauran kasashe a harkokin diflomasiyar kasar a wannan shekara.

Sannan, kasar Sin za ta yi amfani da wadannan taruka wajen ganin an warware matsalolin da duniya ke fuskanta cikin lumana, kamar batun zirin Koriya da rikicin kasar Afghanistan.

Bugu da kari, kasar Sin za ta yi kokarin bullo da matakan bunkasa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da kasashen Amurka da Rasha da kungiyar tarayyar Turai. Za kuma ta karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashe masu tasowa dake yankin Latin Amirka, Afirka da yankin gabas ta tsakiya.

Har ila yau, a tsarin manufar diflomasiyar kasar ta Sin a shekarar 2018, Sin za ta hanzarta aiwatar da ajandar samar da ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030, da bunkasa hadin gwiwa don yakar matsalar sauyin yanayi da ayyukan ta'addanci. Za kuma ta shirya ayyukan sake fasalin yadda ake amfani da Intanet da sararin samaniya cikin lumana.

A shekarar ta 2018, kasar Sin za ta sanya batun aiwatar da yarjejeniyoyin da aka sanya hannu yayin taron dandalin shawarar "ziri daya da hanya daya" da aka gudanar a watan Mayun shekarar da ta gabata, da bullo da matakan bibbiyar ribar da aka samu da kuma matakan kara cin gajiyar hakan.

Sauran fannonin diflomasiyar Sin a wannan shekara, sun hada da samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama, da martaba dokoki da ka'idojin kasa da kasa da na MDD. Masana na cewa, wadannan manufofi sun tabbatar da kudurin kasar Sin na wanzar da zaman lafiya da samun wadata a duniya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China