180212-kokarinta-ya-ba-ta-damar-cimma-burinta-na-wakiltar-Tarayyar-Najeriya-gasar-wasannin-Olympics-na-lokacin-hunturu-Kande.m4a
|
A ranar 6 ga wata ne, aka yi bikin daga tutar Tarayyar Najeriya a tsangayen 'yan wasan Olympics na lokacin hunturu a birnin Pyeongchang da ke kasar Koriya ta Kudu. Seun Adigun mai shekaru 31 da haihuwa, wadda za ta shiga gasar tseren Bobsled, ta yi matukar farin ciki, har ma ta rera waka da rawa tare da masu raye-raye, domin murnar shigar 'yan wasan Najeriya na farko a wasannin Olympics na lokacin hunturu.
Saboda kokarin da ta yi, Adigun ta cimma burin Tarayyar Najeriya na halartar gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu, wannan ya sa an san tutar kasar Najeriya wadda take da yanayi mai zafi a filin wasannin Olympics na lokacin hunturu da ke da matukar sanyi. Sai dai ta shafe shekaru hudu ne kawai wajen cimma wannan babban buri. Masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da labarin Seun Adigun.(Kande Gao)