in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An harba tauraron dan Adam na ba da ilmi a nan kasar Sin mai suna "Shaonianxing mai lamba 1"
2018-02-22 15:40:16 cri

A watan nan na Faburairu ne, a cibiyar harba taurarin dan Adam ta Jiuquan ta kasar Sin, aka harba wani tauraron dan Adam a fannin ba da ilmi na farko mai suna "Shaonianxing mai lamba 1" ta hanyar amfani da rokar dakon kaya samfurin Changzheng 2C. Bayan gwaji da aka yi, tauraron dan Adam din zai samar da bayanai a fannin sadarwa ga makarantun firamare da na sakandare da wasu hukumomin ba da ilmi, wadanda aka kafa rassan binciken tauraron dan Adam a cikinsu, domin ba da hidima ga daliban firamare da na sakandare na kasar Sin wajen samun ilmi a fannin kimiyya da fasahar zirga-zirgar sararin samaniya. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku bayani ne game da wannan ci gaba da aka samu.
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China