in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasannin katun na kasar Sin na neman kasuwannin Afrika
2018-02-03 13:39:51 cri
Kamfanonin kasar Sin sun kaddamar da nazari game da bunkasa wasannin katun a kasashen Afirka a Abuja babban birnin Najeriya, inda a karon farko ake shirin kaddamar da fina-finan katun na kasar Sin a Najeriyar, kasa mafi yawan alumma a nahiyar Afrika.

Manyan kamfanonin shirya wasannin katun na kasar Sin bakwai ne suke Najeriyar, wadanda ke da manufar bunkasa fina-finan katun a Afrika, inda aka fara da Najeriya wacce ta kasance a matsayin babbar kasuwa mafi girma a nahiyar, kamar yadda wakilan kamfanonin shirya wasannin katun na kasar Sin suka bayyanawa taron manema labarai.

Rabiu Adamu, babban jami'i a gidan talabijin na kasa na Najeriya wato NTA, wanda ke hadin gwiwa da kamfanin sadarwa na kasar Sin StarTimes, yace akwai kyakkyawar makoma ga kamfanin dake shirya fina-finan Katun a Najeriya a nan gaba. A cewar Adamu, mafi yawan kananan yara a Najeriya suna kallon shirye shirye na talabijin, sai dai sun fi sha'awar wasannin katun.

Yace suna da bukatar karin shirye shiryen katun na cikin gida, kuma suna fata zasu yi hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin don cimma wannan buri.

A cewarsa suna matukar farin cikin da ziyarar da kamfanonin shirya wasannin na kasar Sin ya kai musu, suna fata zasu samu wasu bangarori da zasu iya yin hadin gwiwa tare domin samar da ingantattun shirye shirye musamman na cikin gida.

Tun da farko a lokacin wata ganawa tsakanin ministan watsa labarai da raya al'adu na Najeriya Alhaji Lai Mohammed, da wakilan kasar Sin, mahukuntan Najeriyar sun bukaci kamfanonin na kasar Sin dasu yi amfani da kyawawan damammakin da gwamnatin Najeriyar ta samar, da suka hada da dage biyan haraji na shekaru 3 ga kamfanonin kasar Sin wanda shi ne matsayi na farko, da kuma zuba jari mai yawa a Najeriyar don samar da kwararru da wadatattun shirye shirye.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China