Da yake tabbatar da hakan a Larabar nan, mataimakin jagoran tawagar Yang Shu'an, ya ce 'yan wasan Sin za su shiga gasanni 55 a rukunoni 12 da za a fafata.
A makamanciyar wannan gasa da ta gabata a birnin Sochi na kasar Rasha, Sin ta samu lambobin zinari 3, da na azurfa 4, da kuma na tagulla 2, wanda hakan ya sanya ta kasancewa kasa ta 12 a kasashe mafiya lashe lambobin zinari a gasar.
Gasar ta 2018 dai za a bude ta ne a ranar 9 ga watan Fabarairu, kuma za a fafata a gasanni 15.