in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira da a yi kokarin samun nasarar yaki da cin hanci da karbar rashawa
2018-01-31 11:01:03 cri

A ranar Litinin da dare ne a hadkwatar kungiyar tarayyar kasashen Afirka AU da ke birnin Addis Ababar kasar Habasha, aka rufe taron kolin kungiyar AU karo na 30. A yayin taron, an tattauna batutuwan da suka jibinci yaki da cin hanci da karbar rashawa da murkushe ayyukan ta'addanci, da dunkulewar kasashen Afirka waje guda.

A ran 29 ga wata da dare ne, a yayin da ake rera taken kungiyar AU "Mu yi murna tare", aka rufe taron kolin kungiyar AU karo na 30 a Addis Ababa bayan da aka yi kwanaki biyu ana tattaunawa kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi kasashen Afirka.

Babban jigon wannan taron koli shi ne "Samun nasarar yaki da cin hanci da karbar rashawa: dauwamammiyar hanyar farfado da nahiyar Afirka." Wannan ne karo na farko da aka mayar da batun kawar da matsalar cin hanci da karbar rashawa a matsayin babban jigon taron kolin kungiyar a cikin shekaru 54 da suka gabata, tun bayan da aka kafa kungiyar hada kan kasashen Afirka kafin daga bisani ta koma kungiyar tarayyar kasashen Afirka.

A yayin taron, a matsayinsa na jagoran jigon taron kolin kungiyar AU ta shekarar 2018, a hukumance shugaban Najeriya Mohammed Buhari ya gabatar da wannan jigo a yayin taron kolin kungiyar AU. A jawabinsa, shugaba Buhari ya jaddada cewa, da farko dai, zai yi kokarin sa kaimi ga matasa da kasashe mambobin kungiyar AU da su aiwatar da "yarjejeniyar AU ta yin rigakafi da yakar matsalar cin hanci da karbar rashawa", ya kuma ba da shawarar kara karfafa dokokin yakar matsalolin cin hanci da karbar rashawa. Sannan shugaba Buhari ya ce, yana da shirin neman abokan aiki daga bangarori daban daban na al'umma. Bugu da kari, yana fatan kwamitin ba da shawarar yaki da cin hanci da karbar rashawa na kungiyar AU ya kara kokari wajen kawar da matsalar a duk fadin Afirka.

A nasa bangaren, shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, ya bayyana cewa, dalilin da ya sa aka mayar da hankali kan matsalar yaki da cin hanci da karbar rasahwa, shi ne matsalar da take tsananta a kai a kai tana kawo illa sosai ga kokarin bunkasa tattalin arziki gami da rayuwar al'ummomi da kuma harkokin siyasa na kasashen Afirka. Mr. Moussa Faki ya nanata cewa, "Ya zama dole mu yi amfani da wannan damar da ake da ita a wannan taron koli domin cimma burinmu na kawar da matsalar cin hanci da karbar rashawa. Dole ne mu dauki kwararan matakan tinkarar matsalar. Ni da shugaba Mohammed Buhari na kasar Najeriya wanda ke shugabancin shirin yakar matsalar cin hanci da rashawa za mu kara hada kai wajen shawo kan wannan matsala. Za mu kara sa ido kan yadda hukumomin kudi ke tafiyar da harkokinsu bisa doka."

Sannan a nasa bangaren, a yayin taron, babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya yi nuni da cewa, MDD da AU za su kara yin hadin gwiwa a fannoni biyar na tabbatar da zaman lafiya da tsaro, da neman samun dauwamammen ci gaba da batun kare 'yancin mata da matasa da 'yan cin rani da batun yakar cin hanci da karbar rashawa, ta yadda za a kara bunkasa dangantakar hadin gwiwa tsakanin MDD da AU. A yayin da ya tabo batun yakar cin hanci da karbar rashawa, Mr. Guterres ya nanata cewa, "Shekarar 2018 shekara ce ta yakar cin hanci da karbar rashawa ta Afirka. Wannan batu na daya daga cikin fannoni biyar da MDD da AU za su yi hadin gwiwa a kai domin tabbatar da dangantakar abokantaka a tsakaninsu. Matsalar cin hanci da karbar rashawa na taimakawa cinikin mutane da miyagun kwayoyi, da kuma satar albarkatun halittu da namun daji, har ma tana lalata sunan gwamnati da kuma kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro. Yanzu MDD na yin hadin gwiwa da hukumomin yakar cin hanci da karbar rashawa na kasashen duniya domin kokarin hukunta wadanda suka aikata ci hanci da karbar rashawa bisa doka."

A taron kolin kungiyar AU na wannan karo ne, aka zabi shugaba Paul Kagame na kasar Rwanda a matsayin sabon shugaban kungiyar AU bisa wa'adin shekara 1. Kuma yana ganin cewa, bai kamata a ci gaba da bata lokaci wajen kokarin dunkulewar kasashen Afirka waje guda ba, dole ne a dauki matakai yadda ya kamata. Shugaba Kagame ya jaddada cewa, "Ya zama dole mu dauki matakan ceton Afirka daga halin da ta dade tana ciki na yadda ake sace albarkatun halittu daga Afirka. Dole ne mu gina wata babbar kasuwar dunkulewar Afirka gu daya, sannan mu yi amfani da fasahohin zamani wajen samar da kayayyakin more rayuwar jama'a masu inganci da bunkasa tattalin arzikinmu. A yau, mun shelanta cewa, za mu kafa wata kasuwar zirga-zirgar jiragen sama daya tilo a Afirka, wannan wani muhimmin mataki ne na kokarin kafa kasuwar zirga-zirgar kayayyaki daya tilo a Afirka. Sannan muna kokarin yin ayyukan share fagen kafa shiyyoyin yin cinikayya marasa shinge a nahiyar Afirka." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China