in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan kasashen duniya za su kara bude kofa, hada kai da kuma amincewa da juna a shekarar 2018
2018-01-31 10:15:38 cri

Jiya Talata ne a nan Beijing, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta shirya liyafar maraba da shigowar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, inda Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da bin hanyar raya kasa cikin lumana.

Yayin da Wang Yi ya waiwayi harkokin diplomasiyyar kasar Sin a shekarar 2017, ya yi nuni da cewa, manufar diplomasiyyar kasar Sin ta biya bukatar bunkasuwar kasar, za kuma ta fara aiwatar da sabbin sauye-sauyen da suka shafi al'amuran kasa da kasa, ta yadda za ta sauke nauyin cika burin kasar Sin na farfado da al'ummar Sinawa, kana ta shiga gwagwarmayar cika burin duniya na samun dawamammen zaman lafiya da wadata ga Bil'adama.

Ministan ya kara da cewa, kasar Sin na fatan ganin a shekarar 2018, kasashen duniya za su kara bude kofa, a maimakon rufe kofa. Kamata ya yi kasashen duniya su kiyaye sabuwar alamar farfadowar tattalin arzikin duniya. Sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare cikin shekaru 40 da suka wuce ya shaida cewa, bude kofa ga duniya, wata hanya ce da ta wajaba wajen tabbatar da samun ci gaba da wadata. Kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga duniya, za kuma ta ci gaba da bude kofarta ga kasashen ketare domin samun moriyar juna da nasara tare.

Wang Yi ya ci gaba da cewa, a shekarar 2018, kasar Sin za ta habaka da zurfafa huldar abokantaka a tsakaninta da abokanta na kasashen duniya daban-daban, za kuma ta hada kai da sassa daban daban wajen warware matsaloli a siyasance wadanda suka dade suna adabar duniya cikin tsawon lokaci. A matsayinta na aminiyar da ake amincewa da ita, kasar Sin za ta ci gaba da taka rawa wajen wanzar da zaman lafiya da bunkasuwa a duniya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China