MDD: A bara sama da mutane miliyan 5.5 sun rasa matsugunnan su a yankin kahon Afirka
Ofishin MDD mai lura da tsare tsaren ayyukan jin kai ko OCHA a takaice, ya ce ya zuwa karshen watan Disambar bara, sama da mutane miliyan 5.5 ne suka rasa matsugunnan su a yankunan kahon Afirka, ciki hadda kimanin mutum miliyan 4.1 da ke gudun hijira cikin kasashen su, da kuma wasu miliyan 1.4 dake neman mafaka a kasashen da ba na su ba.
Wani rahoto da ofishin OCHA ya fitar a Talatar nan, ya bayyana yankin kahon Afirka a matsayin muhimmin zango na 'yan gudun hijira da bakin haure, wadanda ke zirga zirga zuwa zirin kasashen larabawa da na Turai.