in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bai kamata a zargi kasar Sin da laifin ba da kariya ga harkokin ciniki ba
2018-01-25 20:15:54 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta ce, bai dace a zargi kasar Sin da laifin ba da kariya ga harkokin ciniki ba.

Madam Hua ta fadi haka ne a yau Alhamis a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing. Kwanan baya dai, wani jam'in kasar Amurka ya zargi kasar Sin da rashin yakar ba da kariya ga harkokin ciniki ba kamar yadda ta bayyana ba. Madam Hua ta jaddada cewa, shugabannin kasar Sin sun sha nuna cewa, kasar Sin za ta kara bude kofarta ga kasashen ketare. A yayin taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzkin duniya dake gudana a Davos, mamban hukumar siyasa ta kwamitin koli na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kana darektan ofishin kula da harkokin kudi da tattalin arziki na gwamnatin kasar Sin Liu He ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kara kokarin bude kofa ga kasashen ketare, kara ba da iznin shiga kasuwannin kasar Sin, da tsayawa kan kiyaye tsarin daidaita al'amura tsakanin sassa daban daban da tsarin yin ciniki a tsakanin sassa daban daban. Madam Hua ta ci gaba da cewa, kasar Sin na maraba da kasashen duniya da su ci gajiyar saurin bunkasuwar kasar ta Sin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China