A nan kasar Sin, musamman a sassan arewacin kasar, ana fama da tsananin sanyi a lokacin hunturu, duk da haka, sanyin bai hana al'umma su fita daga gida su yi wasanni ba, sanyin da kuma ya samar musu wasu wasanni na musamman masu gwanin ban sha'awa, ciki har da zamiyar wasan kankara, wanda ke matukar samun karbuwa a tsakanin al'ummar Sinawa.