Mai taimakawa ministan kula da harkokin waje da hadin gwiwa da kasa da kasa na hadaddiyar daular Larabawa Mohammed Sharaf ya ce, manufar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje, ba kawai tana taimakawa ga bunkasuwar kasar Sin ba ne, har ma tana amfanar duniya baki daya.
A game da matsalar gurbacewar muhalli da ta sauyin yanayi, tsohon babban sakataren MDD Kofi Annan ya yaba da yadda kasar Sin ta rubanya kokarinta ta fannin magance gurbacewar yanayi, da kyautata muhalli. Ya ce "A ganina, kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa ta fannin sauyin yanayi da kuma muhalli, kuma ina da imanin cewa, gwamnatocin kasa da kasa za su yin koyi da ita." (Lubabatu)