A cewar Adama Barrow, Gambiya na iya koyon nasarorin da kasar Sin ta samu ta fuskar bude kofa ga kasashen ketare. Ya ce, kasar Sin hamshakiyar kasa ce wadda ta iya samun babban ci gaba cikin shekaru kasa da arba'in, balle ma ita kasar Gambiya. Allah ya horewa Gambiya dimbin albarkatu, ciki har da girman kasa, da yankin da take a Afirka, da teku, wadanda dole ne Gambiya ta yi amfani da su.
Adama Barrow ya kara da cewa, bai kamata Gambiya ta gudanar da harkokinta kamar lokacin baya ba, idan har ta ci gaba da bin tsohuwar hanya ba za'a iya cimma burin raya wata sabuwar Gambiya ba.
Har wa yau, Adama Barrow ya shawarci jami'ansa da su nuna jaruntaka gami da zage damtse wajen samun nasara a fannin raya harkokin kasa.
A sau da dama shugaba Adama Barrow na Gambiya ya ambaci saurin bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, musamman bayan da ya ziyarci birnin Beijing a watan Disambar bara.(Murtala Zhang)