in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona a yanki mai zafi ta kasar Sin tana gudanar da hadin gwiwa da kasashen Afirka
2018-01-24 12:00:58 cri

Cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona a yankuna masu zafi ta kasar Sin tana karkashin jagorancin ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, cibiyar ta dukufa kan aikinta na yin nazari kan kimiyya game da aikin gona a yanki mai zafi, har ta fitar da sakamakon da ta samu zuwa ga kasashen Afirka, sassan biyu wato kasar Sin da kasashen Afirka suna gudanar da hadin gwiwa a fannin, haka kuma kokarin da suke ya taimaka matuka wajen samar da tsaron abinci a nahiyar ta Afirka.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, cibiyar nazarin kimiyyar aikin gona a yankuna masu zafi ta kasar Sin tana mai da hankali kan aikin kirkire kirkiren kimiyya da fasaha dake shafar aikin gona a yankuna masu zafi, kana ta taba daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa sama da goma dake tsakaninta da wasu kasashen Afirka kamar su Kwadibuwa da Najeriya da jamhuriyar Kongo, kuma ta kammala aikin gina cibiyar ba da misalin fasahar aikin gona ta kasar Sin a kasar ta jamhuriyar Kongo a shekarar 2009.

Dang Xuanmin, mai yin nazari ne dake aiki a sashen nazarin albarkatun tsirrai na yankin zafi ya taba aiki a cibiyar ba da misalin fasahar aikin gona ta kasar Sin dake jamhuriyar Kongo, yayin aikinsa a kasar, ya yi kokarin koyar wa al'ummun kasar dabarar da ta fi dacewa yadda suke dasa shuke-shuke, kuma ya samu sakamako mai gamsarwa, yana mai cewa, "Bayan kokarin da muka yi, wasu manoman da suka dasa kayan lambu a jamhuriyar kasar Kongo sun kubuta daga kangin talauci, har sun samu wadata. A wancan lokaci, mun yi hayar wasu manoma daga wuraren dake kusa da cibiyarmu ta ba da misalin fasahar aikin gona, mun yi gwaji a gonaki tare da su, makasudin aikinmu shi ne domin koyar musu yadda za su iya yin amfani da dabarar da tafi nagarta yayin da suke shuka tsirrai. Misali yadda ake zuba ruwa cikin gona, aikin yana da muhimmanci, saboda lokacin zuba ruwa, da kuma yawan ruwan da za a zuba, za su kawo babban tasiri wajen girman tsirrai, kana mu kan gaya musu cewa, dole ne a zuba ruwa a hankali, don kada a lalata shuke-shuke."

You Wen, wadda aka haife ta a lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin, ta kammala karatunta na Faransanci a kwalejin koyon harsunan waje ta birnin Dalian na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin a shekarar 2008, har kullum tana kaunar aikin gona, a don haka da zarar ta kammala karatu, sai ta tsai da kuduri cewa, za ta samu wani aikin dake da nasaba da aikin gona a yankin zafi. A shekarar 2011, You Wen ta samu damar yin aiki a cibiyar ba da misalin fasahar aikin gona da kasar Sin ta kafa a jamhuriyar kasar Kongo, ita ma mace ce daya kacal wadda ke aiki a cibiyar, da karo na farko ne ta je nahiyar Afirka, duk da cewa, ta gamu da matsaloli da dama yayin da take aiki a jamhuriyar Kongo, amma ta daidaita dukkansu tare da abokan aikinta, tana mai cewa, "Hakika aikin gona yana da muhimmanci matuka, idan ana gudanar da aikin gona a kasar waje domin samar da taimako ga masu bukata, to, aikin zai fi mallakar ma'ana, ni ma ina sha'awar aikin, shi ya sa ina so in godewa tsarin samar da taimako ga kasashen Afirka da gwamnatin kasar Sin ta tsara, saboda na samu damar ne daga wajen, da gaske ina kaunar aikin, na yi kokari, na samu amincewa daga al'ummun kasashen Afirka."

Bayan kokarin da kwararrun aikin gona na kasar Sin suka yi, al'ummun kasashen Afirka da dama, ciki har da jamhuriyar Kongo suna mallakar fasahar aikin gona ta zamani, hakan ya taimake su matuka wajen samun hatsi mai albarka. Bisa wannan dalilin ne, al'ummun kasashen Afirka sun nuna babbar godiya ga kwararrun aikin gona na kasar Sin, Dang Xuanmin shi ma ya samu tsarabar ban kwana mai daraja da aminansa na kasashen Afirka suka ba shi, yana mai cewa, "Ba zan manta ba har abada, saboda tsarabar ta burge ni kwarai, a wancan rana, dagacin kauyen ya zo wurin da muka sauka da wani katon keke wanda ke cike da 'ya'yan itatuwa da dama, misali kwakwa da gwanda da ayaba, ya ce, 'mun gode muku kwarai, kun zo kasarmu daga kasar Sin mai matukar nisa, domin koyar da mu fasahohi, da tunani, da ilmomi na zamani, ba mu san adadin godiyar da za mu nuna muku ba, kun sani cewa muna fama da kangin talauci, babu abubuwa da yawa, ga shi mun kawo muku 'ya'yan itatuwa masu dadi, muna fatan za ku karba, mu ma muna fatan za ku sake zuwa kasarmu nan gaba, mun gode'."

Tun bayan da kasar Sin ta gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, kwararrun aikin gona na kasar Sin wadanda suka tafi kasashen Afirka domin samar da taimako ga al'ummun nahiyar sun karu sannu a hankali, kokarin da suke ya amfanawa al'ummun kasashen Afirka matuka, kwararrun su ma sun samu sakamako mai gamsarwa daga aikin.(Jamila)


Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China