Da yake jawabi a jahar Sokoto dake arewacin kasar, Ogbonnaya Onu, ya shedawa taron jama'a cewa, za'a iya samar da ayyukan yi sama da 700,000 daga masana'antun sarrafa fatun, ya kara da cewa, masana'antun sarrrafa fatun sun kasance a matsayin wani ginshiki na fadada hanyoyin tattalin arzikin kasar.
A cewar ministan, shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari yana aiki ba kakkautawa wajen inganta cigaban tattalin arziki da kyautata yanayin rayuwar jama'ar kasar ta hanyar karfafa masana'antun cikin gida da fadada hanyoyin tattalin arzikin kasar da kuma kawo sauye sauye a sha'anin tattalin arzikin.
A cewarsa, ma'aikatar zata karfafa gwiwa wajen shigar da 'yan kasar harkokin masana'antu da kuma amfani da fasahohin zamani.
Tun da farko, karamar ministar kasuwanci, masana'antu da zuba jari ta kasar Ai'sha Abubakar, ta shawarci 'yan Najeriya dasu rungumi hanyoyin samun bunkasuwar tattalin arziki ta hanyar kamfanonin sarrafa fatun, kana su bada fifiko wajen sha'awar sayen kayayyakin da aka sarrafa a cikin kasar.