Aiwatar da wannan doka na shaida cewa, kasar Sin ta kawo karshen tsarin karbar kudade kan aikace-aikacen dake gurbata muhalli, wanda aka shafe tsawon shekaru kusan arba'in ana amfani da shi.
Bayanai na nuna cewa, matakan da za'a bi domin tattara haraji sun hada da, na farko gwamnatin lardi za ta bullo da matakan biyan haraji, daga bisani, ta gabatar da su ga majalisar dokokin larduna don samun amincewa, haka kuma za ta gabatar da su ga majalisar dokokin kasa gami da majalisar gudanarwa ta kasar Sin don su tantance. Wata muhimmiyar ka'ida ita ce, idan kamfanoni suka fitar da abubuwa masu gurbata muhalli masu dimbin yawa, za su biya haraji mai yawa. Amma idan suka fitar da abubuwa kalilan, ba za su biya haraji mai yawa ba. Alal misali, idan yawan abubuwa masu gurbata muhalli da wani kamfani ya fitar ya yi kasa da kashi 50 bisa dari na ma'auni harajin, to za'a rage rabin harajin da zai biya. Idan yawan abubuwa masu gurbata muhalli da kamfanin ya fitar ya yi kasa da kashi 30 bisa dari, to zai biya harajin kashi 75 bisa dari.
Nan da shekara daya ko biyu masu zuwa da fara aiwatar da wannan doka, za ta yi tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin, musamman masana'antun da suke gurbata muhalli. Ya zama dole kamfanoni su yi taka-tsantsan, musamman kamfanonin dake fitar da abubuwa masu gurbata iska da ruwa da karar injuna masu damun mutane da sauransu. Wannan mataki ya tilasta wa kamfanonin gaggauta yin kwaskwarima ga ayyukansu, da kara mai da hankali kan ayyukan kare muhalli. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)
180131-Kasar-Sin-ta-fara-aiwatar-da-dokar-biyan-haraji-kan-kare-muhalli.m4a
|