in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron karawa juna sani na kwararrun Sin da Afirka
2018-01-25 17:44:31 cri

A kwanakin baya ne aka bude taron karawa juna sani na kwararrun kasar Sin da kasashen Afrika a birnin Beijing, bisa taken, ci gaban kasar Sin a sabon karni da sabbin damammaki ga hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika.

manufar shirya taron dai ta ce karfafa dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen Afrika da kuma shirye-shiryen gudanar da taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC wanda kasar Sin za ta karbi bakuncinsa cikin wannan shekara.

Cibiyar nazarin kimiyyar zamantakewa ta kasar Sin ce ta dauki nauyin taron, kana cibiyar hadin gwiwar kasa da kasa da nazarin al'amurran kasashen yammacin Asiya da Afrika ta kasar Sin ne ta shirya taron. Kwararru da masana a fannoni da dama na kasar Sin da kasashen Afrika sun gabatar da kasidu a taron.

Masu fashin baki na cewa, taron wata kafa ce ta kara kulla dankon zumuncin tsakanin kasashen biyu, da kuma yadda kasashen Afirka za su kara cin gajiyar ci gaban da kasar Sin ta samu a fannonin rage talauci, raya masana'antu wanda zai kai ga samar da guraben ayyukan yi ga matasan nahiyar da bunkasa aikin gona, tsaro, lafiya da muhimman kayayyakin more rayuwar al'umma. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China