180108-Samun-rancen-yan-kudade-ya-taimakawa-gidan-Yang-Lizhen-wajen-fita-daga-kangin-talauci-Kande.m4a
|
Wmasanin tattalin arziki na kasar Bangladesh Muhammad Yunus, ya taba kafa wani tsarin samar da rancen 'yan kudade a bankin Grameen, lamarin da yasa ya samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekarar 2006 sakamakon amfanawa matalauta. Bisa wannan tsarin, ana iya samar da rancen kudi ga mata, domin samar musu da takamammiyar hanyar dogaro da kansu. A 'yan kwanakin baya, wakilin CRI ya ziyarci kauyen Taiyi na birnin Dali, lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, inda ya ganewa idanunsa kan yadda aka aiwatar da wannan tsarin samar da kananna rancen kudi. Yang Lizhen, wata 'yar kabilar Yi a kauyen tana kokari wajen fitar da kanta har ma da gidanta daga kangin talaucu bisa wannan tsarin. A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar mukuda labarinta.(Kande Gao)