Kakakin hukumar Sami Mshasha, ya bayyana a cikin sanarwar cewa, "duk da matakan da aka dauka na tsuke bakin aljihu, amma hukumar za ta ci gaba da samar da tallafi ga 'yan gudun hijirar Palasdinu, kuma matakin da Amurka ta dauka na daina samar da taimakon kudi ga hukumar ba zai yi tasiri ga wannan alkawarin da hukumar ta dauka ba."
Kakakin ya ce, hukumar za ta dinga samar da tallafi ta fannonin rayuwa da agaji da kiwon lafiya da kuma ilmantarwa ga 'yan gudun hijirar Palasdinu kimanin miliyan 5.9 da suka yi rajista wadanda suka zo daga yamamcin gabar kogin Jordan da zirin Gaza da Syria da Lebanon da kuma Jordan. (Lubabatu)