in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar cinikin waje na kasar Sin a 2017 ta kasance a kan gaba
2018-01-16 12:27:06 cri

Alkaluma sun yi nuni da cewa, a bara wato shekarar 2017, harkokin cinikin waje da kasar Sin ta yi da kasashen waje sun bunkasa inda karuwarsu ta wuce yadda ake zato, abun da ya sa kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa ga farfadowar tattalin arziki da cinikayya na duniya baki daya. Wani babban jami'i a ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, bisa hasashen da aka yi, a bana, cinikin waje na kasar Sin za su ci gaba da bunkasa.

A shekara ta 2017 da ta gabata, jimillar kudaden harkokin shige da fice ta kasar Sin ta kai kusan Yuan triliyan 28, wadda ta karu da kashi 14.2 bisa dari, kana, saurin karuwar ya kasance a kan gaba a cikin jerin shekaru shida da suka gabata.

A nasa bangaren, shugaban sashin kula da harkokin cinikin waje na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Ren Hongbin ya ce, yayin da kasar Sin ke ci gaba da bunkasa harkokin ciniki da Amurka, da tarayyar Turai da kuma Japan, yawan kayayyakin da kasar Sin ta fitar zuwa sauran kasashe ya karu matuka, ciki har da kasashen BRICS, wato Brazil da Indiya da Rasha da Afirka ta Kudu, da kuma kasashen dake cikin shawarar 'ziri daya da hanya daya'. Mista Ren Hongbin ya yi bayani kan musabbabin hakan, inda ya ce:

"Na farko, harkokin kasuwancin duniya ya farfado. Na biyu, tattalin arzikin kasar Sin ya habaka har ya sa aka kara shigo da kayayyaki daga kasashen ketare. Na uku shi ne, manufofin da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta fitar sun kara taka rawa. Na hudu kuwa shi ne, kamfanoni sun kara yiwa tsare-tsarensu gyare-gyare. Na biyar wato na karshe shi ne, yawan kudin cinikin waje da kasar Sin ta samu ya ragu sosai a 'yan shekarun baya, hakan ya kara bada kwarin-gwiwa ga saurin karuwar harkokin shige da fice na kasar Sin a bara."

Jami'in ya kara da cewa, habakar tattalin arzikin kasar Sin cikin tsawon lokaci zai kara janyo jarin waje. Kuma sabuwar kididdigar ta nuna cewa, ana sa ran kasar Sin za ta kasance kasar dake kan gaba a fannin fitar da kayayyakinta zuwa ketare cikin jerin shekaru tara da suka gabata a duk fadin duniya. Tun daga shekara ta 2009 zuwa yanzu, kasar Sin ta zama kasa ta farko da ke fitar da kayayyakinta zuwa ketare, kana, kasa ta biyu da take shigo da kayayyaki daga ketare a duk fadin duniya.

A waje guda kuma, bisa wani sabon rahoton da bankin duniya ya fitar, wato rahoton hangen nesa kan tattalin arzikin duniya a shekara ta 2018, karuwar tattalin arzikin duniya zai kai kashi 3.1 bisa dari a bana. Wasu hukumomin duniya, ciki har da asusun bada lamuni na duniya wato IMF su ma sun bayyana hasashensu mai haske game da habakar tattalin arzikin duniya a bana.

Shugaban sashin kula da harkokin cinikin waje na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Ren Hongbin ya yi hasashen cewa, a bana, harkokin cinikin waje na kasar Sin za su ci gaba da bunkasa, amma ci gabansu zai ragu. Mista Ren ya ce:

"A halin yanzu, ana kara samun farfadowar tattalin arziki a duk fadin duniya, sai dai duk da karuwar bukatar harkokin shige da fice. Amma ana fuskantar wasu abubuwa na rashin sanin tabbas. Akwai wasu kasashen dake bada kariya ga harkokin cinikayya, abun da ya jawo tsaiko ga ci gaban tattalin arzikin duniya. Amma duk da haka, bunkasar tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata zai samar da gishikin ci gaban harkokin shige da fice na kasar. A bana, bisa hasashen da muka yi, harkokin shige da fice na kasar Sin za su ci gaba da habaka, amma saurin ci gabansu zai ragu."

Game da yanayin da tattalin arzikin duniya ke ciki a shekara ta 2018, wasu kungiyoyi gami da hukumomin duniya sun ce, kamata ya yi kasashen duniya su zurfafa gyare-gyare a gida. Kwanan baya, mai magana da yawun hukumar kwastam ta kasar Sin Huang Songping ya bayyana cewa, zai yi wuyar karuwar harkokin cinikin waje na kasar Sin ya wuce kashi goma bisa dari a bana, amma ingancin harkokin zai kara inganta. A cewar Mista Huang:

"Maganar gaskiya ita ce, tattalin arzikin duk duniya zai ci gaba da farfadowa a shekarar da muke ciki. Sa'an nan, tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da habaka yadda ya kamata, abun da zai taimaka ga ci gaban harkokin shige da fice na kasar. Amma saboda karuwar rashin tabbas a duniya, zai yi wuyar ci gaban harkokin shige da fice na kasar Sin ya zarce kashi goma bisa dari a bana. Bisa hasashen da muka yi, a bana, harkokin shige da fice na kasar Sin za su ci gaba da bunkasa yadda ya kamata, kana, ingancinsa zai kara kyautata." (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China