180115-Likitar-kasar-Iran-dake-aiki-a-asibitin-kasar-Sin-Bilkisu.m4a
|
Daraktan sashen kula da kananan yara a wani asibitin mata dake birnin Guangzhou na kasar Sin Yang Hua, ke nan ya gama duba lafiyar wani jariri dan wata guda dan kasar Iran, tare da taimakon wata likita 'yar kasar Iran mai suna Hamini.
"Sunana Hamini, Ni likita ce a sashen gwaje-gwaje na asibitin kula da lafiyar mata na birnin Guangzhou, na fara aiki a nan tun a shekarar 2007. Ban da aikin gwaje-gwaje na yau da kullum, na gano cewa, a 'yan shekarun nan marasa lafiya daga kasashen ketare suna karuwa, kuma na iya Sinanci, Turanci da kuma harshen Persi, hakan yana taimaka musu wajen warware matsalar mu'amala, wannan nauyi ne dake wuya na."
A shekaru 13 da suka wuce, a yayin da take karatu a kasar Malaysia, ta gamu da malam Zhong da ya fito daga kasar Sin, wanda ma ke yin karatu a kasar. Da sauri sun shiga kauna, har ma sun yi aure. Bayan kammala karatu kuma, Hamini ta zo birnin Guangzhou na kasar Sin tare da mijinta don soma aiki da zama a nan.