Umarnin da shugaban ya bayar ya biyo bayan kiraye-kiraye da jama'a ke yi game da yanayin tsaro a jihar ta Benue.
Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya Jimoh Moshood, ya bayyana cewa, tuni aka tura Karin rukunonin 'yan sanda na musamman, da masu yaki da ta'addanci da 'yan sandan yau da kullum zuwa jihar kamar yadda shugaban ya ba da umarni.
Rahotanni na cewa, yanzu haka 'yan sanda sun yi nasarar kama mutane 8 da ake zargi da hannu a munanan hare-haren da aka kai a jihar.
A ranar 1 ga watan Nuwamban shekarar 2017 ne jihar ta Benue ta bullo da dokar hana kiwo a jihar. Dokar tana tanadi daurin shekaru biyar a gidan yari ga duk wanda ya karya ta.
Tun a farkon wannan shekarar ce kashe-kashe da ake zargin Fulani da aikatawa ke karuwa a al'ummomin Logo da Guma dake jihar ta Benue. (Ibrahim)