180103-Wasu-daga-cikin-abubuwan-da-suka-faru-a-duniya-a-shekarar-2017-I.m4a
|
Baya ga ire-iren abubuwan da muka ambata a sama da kan faru a cikin kowace shekara, a kan kuma kulla dangantaka ko kai ziyarar sada zumunci tsakanin manyan jami'ai da shugabannin kasashe da nufin karfafa dankon zumunci ko huldar cinikayya, ko al'adu, ko tattalin arziki da dai sauransu.
Misali, a ranar 8 zuwa 10 ga watan Nuwamban shekarar 2017 ne shugaba Trump na Amurka ya kawo ziyarar aiki kasar Sin, ziyarar da ta janyo hankulan kasashen duniya matuka.
A shekarar ta 2017 ne aka gudanar da zaben shugaban kasa a kasashen Kenya, Rwanda, da Laberiya. Haka kuma a shekarar 2017 da ta gabata ne sojoji a Zimbabwe suka yi wa Robert Mugabe da iyalansa daurin talala, matakin da ya kai ga saukarsa daga mulki, bayan shafe shekaru 37 yana shugabancin kasar. Daga bisani aka rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin shugaban kasa.
Muna fatan samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, alheri da karuwar arziki a duniya baki daya a sabuwar shekara ta 2018.Amin. (Ahmed, Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)