in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bayar da lambobin yabo a fannin kimiyya da fasaha ta shekara ta 2017 a kasar Sin
2018-01-08 18:58:42 cri

Yau Litinin ne, aka yi bikin bayar da lambobin yabo a fannin kimiyya da fasaha ta shekara ta 2017 a birnin Beijing na kasar Sin, inda Wang Zeshan, kwararre a fannin hada albarusai, da Hou Yunde, kwararre a fannin shawo kan yaduwar cututtuka suka samu lambobin yabo da suka fi daraja a wannan fanni.

A yayin bikin, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayar da takardun shaidar lambar yabo ga wadannan kwararru biyu.

Gaba daya aka bada lambobin yabo ga ayyukan binciken kimiyya da fasaha guda 35, da lambobin yabo kan ayyukan kirkire-kirkire guda 66, sa'an nan da lambobin yabo kan ci gaban kimiyya da fasaha guda 170. Har wa yau, akwai masana kimiyya da fasaha daga kasashen waje guda bakwai wadanda suka samu lambar yabo a fannin hadin-gwiwar kasa da kasa ta fuskar kimiyya da fasaha.

A jawabinsa firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada cewa, ya kamata kasar Sin ta kara aiwatar da manufar neman ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China