in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya bayyana muhimman ayyukan diflomasiyya da kasar Sin za ta yi a shekarar 2018
2018-01-08 10:33:56 cri

"Duniyarmu na kasancewa kamar wani babban iyali, kasar Sin tana da nata ra'ayi". A lokacin da yake ambato harkokin diflomasiyya da kasar Sin ke aiwatarwa, a cikin jawabinsa na murnar sabuwar shekara ta 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen kare iko da kuma matsayi na MDD, tana kokarin sauke nauyin kasa da kasa da aka dora mata. Tana kuma cika alkawarin tinkarar sauyin yanayin duniyarmu, har ma tana kokarin mayar da shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta zama gaskiya, domin kokarin zama mai tabbatar da zaman lafiya a duk duniya, kuma mai ba da gudummawa ga ci gaban duk duniya baki daya, har ta zama mai kare odar da ake bi a duk duniya.

Yanzu ga wani rahoto kan yadda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana muhimman ayyukan diflomasiyya da kasar Sin za ta yi a shekarar 2018.

A shekarar 2017 da ta gabata, kasar Sin tana kusan kai cibiyar dandalin duniyarmu a kai a kai. A cikin shekarar, kasar Sin ta kan yi mu'amala da sauran kasashen duniya domin kokarin kara fahimtar juna da yin hadin gwiwa. A kullum, kafofin watsa labaru na kasa da kasa su kan zurar da idanunsu kan manufofi da matakan diflomasiyya da kasar Sin ta dauka. Mr. Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, "A karkashin jagorancin kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, mun yi kokarin aiwatar da jerin sabbin tunani da matakan da shugaba Xi Jinping na kasarmu ya gabatar a cikin shekaru biyar da suka gabata. Mun yi kokarin sabunta matakan ciyar da harkokin diflomasiyya gaba, har ma mun samu wasu muhimman ci gaba da ba mu taba gani ba a da."

A yayin da yake hangen nesa kan muhimman ayyukan diflomasiyya da kasar Sin za ta yi a shekarar 2018, Wang Yi ya nuna cewa, "A cikin rahoton siyasa da shugaba Xi Jinping ya gabata a yayin babban taron wakilan JKS karo na 19, a bayyane take cewa, za a iya yin kokarin kafa sabon salon dangantaka tsakanin kasa da kasa, da kuma kafa wata al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama. Wadannan ayyuka biyu za mu aiwatar da su domin babban burin da za mu yi kokarin cimmawa, a lokacin da muke daidaita harkokin diflomasiyya a nan gaba."

Wang Yi ya yi nuni cewa, ma'anar "kafa sabon salon dangantakar dake tsakanin kasa da kasa" ita ce, neman wata sabuwar hanyar bunkasa dangantakar hulda a tsakanin kasa da kasa. Sannan ma'anar "kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama" ita ce, dole ne a fitar da shirye-shiryen kawar da matsaloli masu tsanani da kasashen duniya ke fuskanta gaba daya. Manyan kasashe sun fi muhimmanci wajen kafa sabon salon dangantakar hulda a tsakanin kasa da kasa. Kaza lika kasar Sin za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa tsakaninta da sauran muhimman kasashe, da gamayyar kasa da kasa na duniya, kamar su kasashen Rasha, da Amurka da Turai, domin kokarin kafa ka'idar bunkasa dangantakar dake tsakanin manyan kasashe, wadda za ta kasance cikin daidaito, kuma ba tare da gargadi ba, ta yadda za a iya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma jituwa a duk duniya gaba daya.

Sannan Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, da farko dai ga kasashe wadanda suke makwabtaka da kasar Sin, sannan ga sauran kasashe masu tasowa. Mr. Wang ya kara da cewa, "Da farko dai, za mu yi kokarin zurfafa dangantakar huldar dake tsakaninmu da kasashe makwabta, ta hanyar ci gaba da nuna abuta su bisa tunanin sada zumunta, da nuna sahihanci da cin gajiya tare, da kuma jurewa juna domin su zama abonkanmu. Za mu yi kokarin shirya dandalin tattaunawa na Bo'ao, da taron kolin kungiyar hada kai ta Shangahai da za a yi a Qingdao kamar yadda ake fata. Bugu da kari, za mu kara zura ido kan matsaya daya da muka samu tare, domin samar da karin karfin fadada hadin gwiwa a yankin da muke ciki."

Bugu da kari, wani muhimmin aikin diflomasiyya da za a yi a shekarar 2018 shi ne shirya sabon taron kolin dandalin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka, wato FOCAC. Wang Yi ya bayyana cewa, bangaren Sin zai hada shawarar "ziri daya da hanya daya" da ajandar Afirka nan da shekarar 2063, ta yadda shawarar "Ziri daya da hanya daya" za ta zama wani sabon karfin bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka daga dukkan fannoni.

Bisa bayanin da aka bayar, an ce kawo yanzu, kasar Sin da sauran kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 80, sun riga sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", a yayin da take yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya fiye da 30 a fannin kere-kere da samar da makamashi.

Mr. Wang Yi, ministan harkokin wajen kasar Sin ya nuna cewa, a shekarar 2018, kasar Sin za ta yi kokarin fadada tsarin kulla abuta a duk duniya, domin ci gaban aikin kafa sabon salon dangantakar huldar dake tsakanin kasa da kasa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China