A Larabar nan 3 ga wata ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron manema labaru cewa, kasar Sin na tinkarar al'amuran kasa da kasa bisa ka'idar yin shawarwari tare, da raya duniya tare, da cin moriyar bunkasuwar duniya tare. Kuma ko kadan ba ta da nufin yin jagoranci ko kuma maye gurbin wata kasa, yayin da ake tinkarar al'amuran duniya.
An labarta cewa, a kwanan baya, dandalin masana na kasar Amurka karkashin kamfanin Eurasia ya ce, a shekarar 2018, duniya za ta ci gaba da fuskantar koma-baya a fannin siyasa. Kuma kasar Sin tana yunkurin maye gurbin Amurka a wasu al'amuran duniya, wanda shi ne kalubale mafi tsanani a duniya a bana. (Tasallah Yuan)