in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Zambia ya yi murabus
2018-01-03 11:46:44 cri
Ministan harkokin kasashen waje na kasar Zambia Harry Kalaba ya sanar da yin murabus daga mukaminsa. Cikin wani sako da Kalaba ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce ya dauki wannan mataki ne sakamakon abin da ya kira, garazawar gwamnati wajen yakar jami'anta dake satar kudaden al'umma da kuma matsalar cin hanci da rashawa.

Sai dai kuma Mr. Kalaba ya ce zai ci gaba da zama mamba a majalisar dokokin kasar karkashin inuwar jam'iyya mai mulki. A ranar Litinin ne dai, Kalaba ya wallafa wata sanarwa a shafinsa na Facebook, inda ya bankado badakalar karuwar cin hanci a shekarar 2017, sanarwar da ta girgiza wasu 'yayan jam'iyyar,da har wasu ke kiran da ya yi murabus.

Koda yake kakakin shugaba Edgar Lungu na Zambia, Amos Chanda ya shaidawa kafofin watsa labaran kasar cewa, har yanzu fadar shugaban kasar ba ta karbi takardar yin murabus din tasa ba.

Mr Kalaba dai ya shafe sama da shekaru hudu yana rike da wannan mukami.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China