in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu ingantuwar gidajen kula da tsofaffi a kasar Sin a shekarar 2017
2018-01-03 10:28:08 cri
Ministan harkokin cikin gida na kasar Sin Huang Shuxian ya bayyana cewa, kasarsa ta inganta cibiyoyin kula da tsofaffi a karshen watan Nuwanban shekarar 2017 da ta shude.

Ministan wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, ya ce, an samar da kayayyakin kiwon lafiya a kaso 93.4 cikin 100 na dukkan gidajen kula da tsofaffi. Haka kuma ya zuwa karshen watan Nuwamban shekarar 2017 an kara adadin gadajen da ake samarwa don amfani tsofaffin da ba sa iya kula da kansu daga kasa da kaso 30 cikin 100 a shekarar 2015 zuwa kaso 46.4 cikin 100.

Huang ya kara da cewa, akwai sama da cibiyoyin kula da tsofaffi 28,000 da aka yiwa rijista a fadin kasar, kuma suna da gadaje kimanin miliyan 7 a watan Satumban shekarar 2017. Sai dai kuma sama da irin wadannan cibiyoyin kula da tsofaffi 12,500 masu zaman kansu ne, karin sama da kaso 7.8 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara.

Bayanai na nuna cewa, a karshen shekarar 2016 akwai mutane miliyan 230 masu shekaru 60 zuwa sama a kasar Sin, kaso 16.7 cikin 100 na yawan al'ummar kasar. Daga cikin wannan adadi kaso 51.3 cikin 100 tsofaffi ne wadanda ke zama ba tare da 'yayansu ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China