in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar kare namun daji ta Uganda ta yaba matakan Sin na haramta cinikin haurin giwa
2018-01-03 10:21:03 cri
Hukumar kare namun daji ta kasar Uganda(UWA) a takaice ta bayyana cewa, matakan da mahukuntan kasar Sin suka dauka na haramta cinikin haurin giwa wani babban ci gaba ne, wadda kuma ta yaba da shi matuka.

Babban darektan hukumar Andrew Seguyam wanda ya bayyana hakan yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce, shawarar da kasar Sin ta yanke na haramta cinikin haurin giwan, zai taimaka wajen kare giwayen Uganda da na Afirka da ma wadanda ke sassa daban-daban na nahiyar Afirka.

A ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2017 ne, mahakuntan kasar Sin suka haramta ciniki ko sarrafa haurin Giwa da ma abubuwan da aka yi daga gare shi a fadin kasar.

Alkaluman da kungiyar kare muhallin halittu ta duniya ta fitar na nuna cewa, yawan giwaye a nahiyar Afirka ya ragu da 111,000 cikin shekaru goman da suka gabata. Kana yadda ake farautar giwaye a nahiyar shi ma ya ragu matuka tun daga shekarar 2011, amma har yanzu al'amari bai canja ba a nahiyar baki daya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China