Wata takarda da kotun kolin ta fitar a jiya Talata, ta ce, an bukaci kotuna su yi amfani da matsayinsu wajen kare muradun masu masana'antu kamar yadda doka ta tanada, muddin masana'antun da kirkire-kirkiren wajen samar da kayayyaki da yadda suke tafiyar da harkokin kudi ba su saba dokoki ba.
Bugu da kari, sanarwar ta bukci kotunan da su bambance tsakanin kayayyakin da doka ta amince da ribar da ta sabawa doka da masana'antun ke samu.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa,wajibi ne kotunan su kare muradun halal na masana'antun, sannan su hukunta bata gari bisa tsarin doka. (Ibrahim)