in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummun Zimbabwe suna sa ran za a samu ci gaban tattalin arziki a kasarsu
2017-12-27 10:44:04 cri

Ranar 15 ga watan Nuwamban bana, sojojin kasar Zimbabwe sun tsare shugaban kasar na wancan lokaci Robert Mugabe da iyalansa, bisa dalilin cewa suna farautar masu aikata laifuffuka dake kusa da shugaban kasar. A sanadin hakan, an tumbuke Mugabe wanda ke rike da jagorancin kasar har tsawon shekaru 37, kuma Emmerson Mnangagwa ya hau kujerar shugabancin kasar. To ko an fitar da wasu sabbin manufofi a kasar a cikin wata guda da ya gabata?

Filin gonar shukka ciyayin samar da taba na Danford Mutwiwa yana yankin kudu maso gabashin birnin Harare, fadar mulkin kasar ta Zimbabwe. Tun daga shekarar 2004, wato tun bayan da aka gudanar da kwaskwarima kan ikon mallakar gonaki a kasar, sai Danford ya fara shuka ciyayin samar da taba a wurin, kuma filin gonarsa ya habaka sannu a hankali karkashin taimakon wani kamfanin kasar Sin. A baya fadinsa bai wuce hekta 7 kacal ba, amma yanzu ya riga ya kai hekta 220. Danford ya nuna fatansa ga sabuwar gwamnatin kasarsa, yana mai cewa, yanzu farashin kayayyaki a kasar ya karu bisa babban mataki, wanda hakan ya kawo babbar illa ga kasuwancinsa. Manomin na fatan sabuwar gwamnatin za ta fitar da sabbin manufofi domin kara janyo jarin da za a zuba, tare kuma da kyautata yanayin tattalin arzikin da kasar ke ciki, ya ce, "Daga halin da muke ciki yanzu, mun lura cewa, ko shakka babu sabuwar gwamnatin za ta fitar da wasu sabbin manufofi, idan tattalin arzikin kasarmu ya samu ci gaba, hakan zai amfani sana'ar samar da taba da muke yi, muna bukatar manufar da ta dace domin goyon bayan ci gaban aikin gona a kasarmu. Yanzu haka farashin kayayyaki yana da tsada matuka a kasarmu, a saboda haka muna fuskantar matsaloli da dama, muna fatan sabuwar gwamnati za ta fitar da manufofin sa kami ga zuba jari."

Ra'ayin da dama daga jama'ar kasar, dalilin da ya sa aka tumbuke Mugabe daga mukaminsa shi ne yanayin siyasa da kasar ke ciki na da tangarda, kana tattalin arzikin kasar bai samu ci gaba yadda ya kamata ba, shi ya sa ya zama dole sabuwar gwamnatin kasar ta Zimbabwe ta kara mai da hankali kan aikin raya tattalin arziki a kasar. A ranar 24 ga watan Nuwamban da ya gabata, sabon shugaban kasar Mnangagwa ya bayyana yayin bikin rantsuwarsa cewa, gwamnatin kasarsa za ta mayar da aikin farfadowar tattalin arziki a matsayin koli, ta yadda za a samar da guraben aikin yi da wadata ga al'ummun kasar, wadanda suke shan wahalhalun talauci a cikin shekaru sama da goma da suka gabata.

A ranar 7 ga wata, ministan kudin kasar Patrick Chinamasa ya gabatar da wani rahoto ga majalisar dokokin kasar, inda ya fitar da kasafin kudin kasar na shekarar 2018, a cikin rahoton, abu mafi jawo hankalin jama'a shi ne kasar za ta yi wa tsarin mallakar filayen kasar gyaran fuska, Chinamasa ya ce, "Za a ci gaba da aiwatar da dokar sayen hannun jari a fannin sana'ar hakar ma'adinan lu'u lu'u da Platinum, wato dole ne bakaken fata mazaunan kasar su mallaki hannun jarin sama da kaso 51 bisa dari. Game da sauran sana'o'in hakar ma'adinai kuwa, ba za a hana kowa sayen hannun jarin ba."

Ban da haka kuma, sabuwar gwamnatin za ta dauki wasu matakai domin rage kudaden da za ta kashe, mai jagorancin kungiyar 'yan kasuwar kasar Zimbabwe Matunda Mugaga ya bayyana cewa, a takaice dai ana iya cewa, rahoton nan na kasafin kudi ya nuna mana cewa, kasar ta Zimbabwe za ta sanya kokari matuka domin raya tattalin arziki, ya ce, "Ina ganin cewa, wannan rahoto na kasafin kudi zai sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki a kasar, duba da cewa, an fitar da wasu sabbin manufofi, yanzu haka, muna cike da imani kan makomarmu a nan gaba."

Domin taimakawa kasar ta Zimbabwe, kasashen duniya su ma sun samar da taimako. A ranar 6 ga wata, gwamnatocin kasashen Sin da Zimbabwe sun daddale yarjejeniyoyi guda uku dake tsakaninsu a birnin Harare, inda gwamnatin kasar Sin ta yi alkawari cewa, za ta samar da rancen kudi mai gatanci ga gwamnatin Zimbabwe, kuma za ta kara samar da taimako gare ta ba tare da gindaya sharadi ba, domin gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a a kasar, misali filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Robert Mugabe, da sabon ginin majalisar dokokin kasar da sauransu. A ranar 13 ga wata, bankin shige da fice na Afirka shi ma ya sanar da cewa, zai samar da rancen kudi har dalar Amurka biliyan 1 da miliyan 500 ga kasar domin kiyaye zaman karko na tattalin arziki a kasar.

Bayan da shugaba Mnangagwa na kasar ya fara jagoranci a kasar, sai ya bukaci ministocin kasar da su dauki matakai cikin gajeren lokaci su dauki matakan farfado da tattalin arziki a kasar, tare kuma da kyautata rayuwar al'ummun kasar. Ana sa ran cewa, kasar za ta samu sakamakon da al'ummun kasar suke fata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China