in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kakabawa wasu mutane 2 'yan koriya ta arewa takunkumi
2017-12-27 09:44:01 cri
Amurka ta sanyawa wasu mutane biyu 'yan kasar Koriya ta arewa takunkumi, bisa zarginsu da hannu cikin shirye-shiryen makamai masu linzami na kasarsu.

A cewar baitul malin Amurka, bisa wannan mataki, za a dakatar da su daga amfani da duk wata kadara ko dukiyarsu dake Amurka, sannan an haramtawa Amurkawa cinikayya da mutanen.

Zaman dar-dar a zirin Korea ya kai wani mataki da ba a saba gani ba a bana, inda Koriya ta arewar ta yi gwajin nukiliya da makamai masu linzami, yayin da Amurka da Koriya ta kudu ke ta gudanar da atisayen soji. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China