Mr.Lavrov ya yi wannan furuci ne a yayin da yake karbar tambayoyin da gidan talabijin na RT na kasar ya yi masa a wannan rana.
A ranar 29 ga watan Nuwanba, kasar Koriya ta arewa ta sake gwajin harba makamai masu linzami. A ranar 22 ga wata kuma, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri na kakabawa Koriya ta arewa takunkumi, takunkumin da ya shafi fannonin man fetur, da kwadago, da abinci, da injuna, da kayayyakin lantarki da katako da sauransu.(Lubabatu)