Kwanan nan ne jami'an diplomasiyyar da suka zo daga wasu kasashe bakwai, ciki har da Mr. Sidibe Mohamadou Aboubakar jami'in kula da harkokin watsa labarai a ofishin jakadancin jamhuriyar Nijer da ke kasar Sin, da uwargidansa Idrissa Balkissa, da ma sauran jami'an diplomasiyya da suka zo daga kasashen Afghanistan, da Brazil, Cambodia da sauransu, suka kai ziyara lardin Jiangsu na kasar Sin. Sun kai ziyara lardin Jiangsu na kasar Sin ne bisa ga goron gayyatar da gidan rediyon kasar Sin CRI ya ba su. A tsawon kwanaki shida da suka shafe suna wannan ziyara, sun ziyarci biranen Nanjing da Zhenjiang da kuma Taizhou dake lardin na Jiangsu, inda suka gane wa idonsu bunkasuwar lardin, da dadadden tarihinsa, da kuma wurare masu ni'ima. Bayan kammala ziyarar, mun samu damar tattauna da malam Sidibe da uwargidansa, dangane da abubuwan da suka gani a yayin ziyarar, ga kuma yadda hirar ta kasance.
171215-ziyarar-jamian-diplomasiyya-a-lardin-jiangsu-na-kasar-sin-Lubabatu.m4a
|