in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bikin kasa na tunawa da kisan kiyashi na birnin Nanjing
2017-12-14 13:29:28 cri

Jiya ranar 13 ga watan Disamba, ranar cika shekaru 80 ce tun bayana kisan kiyashi a birnin Nanjing na kasar Sin. A safiyar jiya, an gudanar da bikin kasa na tunawa da kisan kiyashi a birnin, wanda ya samu halartar babban sakataren JKS, shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiyar JKS Xi Jinping.

An gudanar da bikin kasa na tunawa da kisan kiyashi ne a filin dake gaban babban dakin tunawa da Sinawan da suka rasa rayukan su a yayin kisan kiyashin da sojoji mahara na kasar Japan suka yi a birnin Nanjjing na lardin Jiangsu dake kudancin kasar Sin, inda aka sassauto da tutar kasa kasa kasa, domin isar da alhini ga Sinawan da sojoji mahara na Japan suka kashe.

Yayin bikin kasar, wakilan da suka zo daga bangarori daban daban sama da dubu goma, sanye da furanni masu launin fari a kirjinsu sun tsaya shiru a dandalin. Da misalin karfe 10 da safe, shugaban kasar Xi Jinping da sauran shugabannin kasar sun shiga filin inda suka tsaya a gaban wakilan.

A ranar 13 ga watan Disamban shekarar 1937, sojoji mahara na kasar Japan sun kutsa cikin birnin Nanjing, suka kuma yi kisan kiyashi, inda suka kashe Sinawa dubu 300, tare da aikata mumunan laifin cin zarafin bil adama, masifar da ta kawo bakin ciki mai tsanani ga al'ummar kasar Sin, wadda ba za su manta ta ba har abada.

A watan Faburairun shekarar 2014, hukumar dokoki ta kasar Sin ta zartas da kuduri, inda aka kebe ranar 13 ga watan Disamban ko wace shekara, a matsayin ranar duk kasa ta tunawa da 'yan kasar da aka kashe a yayin kisan kiyashi na birnin Nanjing.

An fara bikin da misalin karfe 10 na safe, kuma wakilai a filin sun rera taken kasar Sin da babbar murya, daga baya sun mike tsaye suka yi shiru dan lokaci domin nuna juyayi, a sa'i daya kuma, an busa jiniyar gargadin harin sama a fadin birnin na Nanjing. Motoci da jiragen kasa, da jiragen ruwa su ma sun busa jiniyar gargadin aukuwar wannan hari, al'amarin tamkar dakatar da lokaci ne, daukacin Sinawa suna bakin ciki, suna tunawa da 'yan uwa da suka rasa rayukansu, a yayin kisan kiyashi na Nanjing, inda suke tunawa da dukkan 'yan uwa, da sojoji mahara na kasar Japan suka kashe a fadin kasar.

Yayin bikin, wakilan matasa da yara na birnin Nanjjing da yawansu ya kai 80 sun karanta "sanarwar zaman lafiya".

Shugaban majalisar ba da shawata kan harkokin siyasa ta kasar Sin wanda ya halarci bikin Yu Zhengsheng ya bayyana cewa, muddin dai an fahimci tarihi, za a iya samun makoma mai haske, a saboda haka bai kamata a manta da tarihi ba, kana bai kamata mu manta da labaran kaka da kakkaninmu ba. Haka kuma domin gujewa sake aukuwar wannan masifar, ya dace mu yi kokari tare, ta yadda za mu shimfida zaman lafiya a fadin duniya. Domin cimma wannan buri, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa hanyar zaman lafiya, ba za ta nuna karfin tuwo ba, kuma har abada ba za ta kai hari ga wasu kasashe ba.

Kafin a kammala bikin, wakilai 6 sun kada babban agogon zaman lafiya tare, har sau uku.

Har ila yau, an saki tsuntsayen kurciyoyi 3000 masu alamar zaman lafiya sama. Ana tunawa da wadanda suka rasa rayukansu yayin kisan kiyashin Nanjing dubu 300, kuma ana fatan kasar Sin za ta kara karfi daga duk fannoni yadda ya kamata.

Bayan bikin, shugaba Xi Jinping ya gana da wakilai mazauna birnin Nanjing, wadanda suka tsira da rayukan su a masifar, da wasu wakilan dangogin aminai na kasa da kasa, wadanda suka ba da gudumowa a yayin yakin da aka yi da maharan Japan, inda aka gabatar musu fatan alheri, tare kuma da nuna fatansa cewa, za su ji dadin zaman rayuwa, ya ce, "Ina fatan za ku ci gaba da jin dadin zaman rayuwa, kuma ina fatan ku rika tunawa da masifar kasarmu, kada ku manta."

Shugaba Xi ya kara da cewa, tarihi yana da muhimmanci matuka gare mu, ya zama wajibi mu tuna da tarihi na gaske, saboda tarihi tamkar madubi ne, kamata ya yi mu waiwayi tarihi yayin da muke kokarin samun ci gaba, ya ce, "Al'amuran da suka faru a tarihi suna da muhimmanci matuka gare mu yayin da muke kokarin samun ci gaba a halin yanzu, saboda muna iya samu fasahohi daga tarihi, da haka za mu iya samu hanyar da ta dace mu bi a nan gaba."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China