in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi maraba da muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa kan batutuwan da suka shafi duniya
2017-12-13 13:49:56 cri
Shugaban zauren MDD na 72 Miroslav Lajcak, ya ce ya yi maraba da muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa a yanzu, wajen jagorantar batutuwan da suka shafi kasa da kasa.

Miroslav Lajcak, ya bayyana cikin wata tattauanwa da Kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Kasar Sin ta riga ta mamaye wani muhimmin mataki a matsayinta na daya daga cikin mambobin dindindin na kwamitin sulhu na MDD, kana ta zama daya daga cikin manyan masu bada gudunmuwa ga kasafin kudi da samar da kudaden raya majalisar.

Ya ce kasar Sin na daya daga cikin kasashen farko da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris, sannan ta yi alkawarin bada dala biliyan 3.1 ga asusun hadin gwiwa na tallafawa kasashen maso tasowa magance sauyin yanayi wato South-South Cooperation Fund, wanda ke matsayin wani muhimmin yunkuri ga kasashe masu tasowa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China