Jakada Liu na maida martani ne game da zargin da wasu kafafen watsa labaru na kasashen yammacin duniya ke yayatawa a baya bayan nan, cewa kasar ta Sin na yin kutse cikin al'amuran dake wakana a wasu kasashen Afirka.
Cikin wata makala da aka wallafa a mujallar Daily Telegraph, Jakada Liu Xiaoming, ya ce ita kan ta kasar Sin ta fuskanci kutse daga wasu kasashe a tarihin ta, wanda hakan ya sa bata taba sha'awar yin haka ga wata kasa dake Afirka ba.
Ya ce burin Sin shi ne musayar kwarewa tare da takwarorin ta na Afirka, kuma a shirye take, da ta gudanar da musayar ra'ayi da kasashen nahiyar, ta yadda hakan zai bude hanyoyin bunkasa ci gaban yanayin siyasa a nahiyar.
Daga nan sai jakadan na Sin wanda a baya ya yi aiki a ofisoshin jakadancin wasu kasashen Afirka 2, ya jaddada manufar kasar Sin ta tallafawa kasashen Afirka ta hanyoyin da duk suka dace, ba tare da gindaya wani sharadi ba.
Ya ce burin Sin bai wuce bada gudunmawa wajen inganta rayuwar al'umma, da raya kasashen Afirka ba.




