171213-Rawar-da-Intanet-ke-takawa-ga-ci-gaban-tattalin-arziki-a-duniya.m4a
|
A yayin taron na yini uku wanda shi ne na hudu a jeren tarukan da ake gudanarwa, za a gabatar da rahoton ci gaban da aka samu a harkar yanar gizo na duniya na shekarar 2017, da kuma rahoton raya harkokin yanar gizo na kasar Sin na shekarar 2017, wadanda za su shaida yadda yanar gizo ke samun bunkasuwa a kasashen duniya, da kuma yanayin bunkasuwar yanar gizo da makomarta a kasar Sin.
Bugu da kari, a yayin taron, an baje kolin kayayyakin yanar gizo, inda manyan kamfanonin yanar gizo da sabbin kamfannonin kirkire-kirkire fiye da 400 suka nuna sabbin fasahohin zamani daban-daban na yanar gizo da aka samu a duniya.
Masana na fatan taron na bana, zai kara bullo da matakan tsaron intanet, da rawar da Intanet ke takawa ga ci gaban tattalin arziki, da samar da guraben aiki yi tsakanin matasa a duniya. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)