in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ko rikicin yankin Gabas ta tsakiya zai kara tsananta sakamakon matakin gwamnatin kasar Amurka na sauya manufarta game da yankin?
2017-12-07 10:54:53 cri

A jiya Laraba ne, shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya shelanta cewa, gwamnatinsa ta amince da birnin Kudus a matsayin fadar mulkin kasar Isra'ila, duk da rashin amincewa da kasashen dake yankin Gabas ta tsakiya da kasashen Turai suka nuna kan matakin na Amurka. Shugaba Trump ya cika alkawarin da ya yi ne a lokacin da yake yakin neman zaben shugabancin kasar Amurka, a waje daya kuma, ya yi watsi da manufar kasar Amurka na shekaru da dama, kana ya shure matsayar daya da al'ummomin duniya suka cimma kan batun matsayin birnin Kudus, mataki da mai yiyuwa ya kara tsananta halin da ake ciki a yankin.

"Yanzu lokaci ne a amincewa da birnin Kudus a matsayin fadar mulkin kasar Isra'ila a hukumance."

Da misalin karfe 1 na yammacin jiya Laraba ne, shugaba Trump ya gabatar da wani jawabi a fadar White House kan batun matsayin birnin Kudus, inda ya ce, ya amince da hakikanin halin da ake ciki ne kawai. A waje daya, ya jaddada cewa, kasar Amurka tana goyon bayan shirin kafa kasashe biyu kamar yadda ta yi a da.

"Ba mu da kowane irin matsayi kan batun matsayin karshe na birnin. Kawo yanzu, kasar Amurka tana kokarin taimakawa bangarori biyu wajen amincewa da wata yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu. Idan bangaori biyu suka yarda, kasar Amurka za ta ci gaba da tsayawa kan shirin kafa kasashe biyu."

A matsayin wuri mai tsarki ga Yahudawa da Kiristoci da kuma na Musulumi, batun matsayin birnin Kudus na daya daga cikin batutuwa masu muhimmanci da yake ta da hankali tsakanin Palesdinu da Isra'ila. A kullum kasashen duniya suna ganin cewa, ya kamata bangarorin biyu su daidaita batun ta hanyar yin tattaunawa cikin lumana. Har yanzu babu wata kasa da ta bude ofishin jakadancinta a birnin Kudus.

Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, batun matsayin birnin Kudus ya kawo baraka tsakanin manyan jami'an gwamnatin kasar Amurka. Mr. Rex Tillerson, sakataren harkokin wajen kasar Amurka da Mr. James Norman Mattis, sakataren tsaron kasar Amurka da Mike Pompeo, shugaban hukumar leken asiri ta kasar Amurka ba su yarda da kasar Amurka ta canja manufarta kan batun matsayin birnin Kudus ba. Har ma Mr. John Brennan, tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasar Amurka ya fitar da wata sanarwa, inda ya ce, shugaba Trump ya tsai da wani kuduri da bai dace ba, domin zai kawo illa ga muradun Amurka a yankin Gabas na tsakiya. Amma mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence, da jakadar kasar Amurka dake MDD madam Nikki Haley da jakadan kasar Amurka dake Isra'ila sun goyi bayan matakin da shugabansu ya dauka.

Bugu da kari, ko da yake a ran 5 ga wannan watan, shugaba Trump ya buga waya ga shugabannin kasashen Isra'ila da Palesdinu da Jordan da Masar da kuma na Saudiyya, amma ban da gwamnatin Isra'ila, sauran kasashen Larabawa da na Turai dukkansu sun nuna adawa da kudurinsa.

A bangaren MDD, bayan da shugaba Trump na kasar Amurka ya bayyana kudurinsa game da batun birnin Kudus, nan take, Mr. António Guterres, babban sakataren MDD a jawabin da ya gabatar, ya nuna adawa da dukkan matakin da bangare daya tilo ya dauka na kawo barazana ga kokarin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya. Yana fatan bangarorin Palesdinu da Isra'ila za su gaggauta komawa kan teburin yin shawarwari. Mr. António Guterres ya ce, "Tun a kwanankin farko bayan da na kama aikin babban sakataren MDD, a kullum ina nuna adawa da dukkan matakan da bangare daya tilo ya dauka na kawo barazana ga kokarin shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinu da Isra'ila. Dole ne bangarorin Palesdinu da Isra'ila su tabbatar da matsayin karshe na birnin Kudus ta hanyar yin shawarwari cikin lumana bisa kuduran da aka zartas a yayin tarukan kwamitin sulhu da na babban taro na MDD a lokacin da ake tattara ra'ayoyin daidaikun Palesdinu da Isra'ila."

A waje daya, Mr. António Guterres ya bayyana cewa, a matsayinsa na babban sakataren MDD, zai yi duk kokarin da ya dace na goyon bayan yin shawarwari mai ma'ana tsakanin shugabannin Palesdinu da Isra'ila domin cimma burin shimfida zaman lafiya a tsakaninsu har abada. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China