Ranar 1 ga watan Disamba, rana ce ta yaki da cutar kanjamau ta duniya karo na 30. Kamar yadda aka sani ne, cutar kanjamau ta kasance mummunar cutar dake kawo barazana ga lafiyar jama'a. Kuma har yanzu babu maganin wannan cutar, sai dai allurai ko kwayoyin rage kaifin cutar har tsawon rayuwa. A nan kasar Sin, ya zuwa watan Yuni na shekarar bana, yawan wadanda suka kamu da cutar kanjamau sun kai dubu 718, kuma an fi saurin yada cutar ta hanyar jima'i. Ban da wannan kuma, ana samun saurin yaduwar cutar a tsakanin dalibai matasa da tsofaffi. Kwararrun sun bayyana cewa, kamata ya yi a kara ilmantar da jama'a a fannin jima'i a makarantu, don rage yadda dalibai ke kamuwa da cutar. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu kawo muku bayani ne game da wannan batun.
171204-Kasar-Sin-na-kara-matakan-ilmantarwa-yara-a-fannin-ilimin-jimai-a-makarantu-don-tinkarar-cutar-kanjamau-Bilkisu.m4a
|