in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da babban taron intanet na kasashen duniya karo na 4 a kasar Sin
2017-12-04 11:05:06 cri

Jiya Lahadi ne, aka kaddamar da babban taron intanet na kasashen duniya karo na 4 a garin Wuzhen na lardin Zhejiang dake kudu maso gabashin kasar Sin, inda mahalartan taron da suka zo daga kasar Sin da kuma kasashen ketare za su tattauna kan ci gaban tattalin arzikin da ake samu ta hanyar amfani da fasahohin zamani a fadin duniya.

A kan shirya babban taron intanet na kasashen duniya ne sau daya a kowace shekara, kawo yanzu an gudanar da taron har sau uku, babban taken taron na bana shi ne "bunkasa tattalin arziki ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani tare kuma da sa kaimi kan morewar juna ta hanyar bude kofa, ta yadda za a samar da kyakkyawar makoma ga daukacin bil adama kan yanar gizo."

Shugaban rukunin Inspur wanda ke kan gaba a fannin samar da hidima ta yanar gizo Sun Pisu ya bayyana cewa, batun yadda ake hada tattalin arziki kan intanet da bangaren tattalin arziki dake samar da kayayyaki da hidima, shi ne batun da ya fi jawo hankalin al'ummun kasashen duniya, a baya, ba a hada fasahohin zamani da tsoffin ayyuka sosai, amma yanzu yanayin ya sauya, Sun Pisu ya ce, "A halin da ake ciki yanzu, kamata ya yi a yi amfani da fasahohin zamani domin kyautata tsoffin ayyuka, ko kuma kyautata bangaren tattalin arziki dake samar da kayayyaki da hidima, haka zai sa a iya samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri daga duk fannoni, ana iya cewa, akwai bukatar a hada sabbin fasahohi da sabbin ayyuka da bangaren tattalin arziki dake samar da kayayyaki da hidima yadda ya kamata."

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, harkokin tattalin arziki ta intanet ya kasance muhimmin bangaren tattalin arziki a kasar Sin, inda adadinsa ya kai RMB yuan biliyan dubu 22 da dari hudu a shekarar 2016 da ta gabata, saurin karuwarsa ya kai kaso 16.6 bisa dari, saurin da ya fi saurin karuwar GDP na kasar, kana adadin ya kai kaso 30.1 bisa dari na GDPn kasar a duk shekarar bara. Ban da haka adadin ya kai matsayi na biyu a duniya, saurin karuwarsa ya kai matsayin koli a fadin duniya.

Kwararren cibiyar injiniya ta kasar Sin kuma shugaban kungiyar intanet ta kasar Sin Wu Hequan yana ganin cewa, nan gaba tunanin bude kofa da kirkire kirkire zai taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban harkokin tattalin arziki ta yanar gizo, ya ce, "Ci gaban tattalin arziki ta yanar gizo yana da muhimmanci matuka ga ci gaban zaman takewar al'umma, haka kuma yana shafar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen duniya, a saboda haka wajibi ne a bude kofa ga kasashen ketare ban da haka kuma kirkire kirkire shi ma yana da muhimmanci, saboda yanayin da kasar Sin ke ciki ya sha bamban da na sauran kasashen duniya, shi ya sa ya zama dole mu yi kokarin raya tattalin arziki bisa tsari mai halayyar musamman ta kasar Sin."

Batun samar da kyakkayar makoma ga dukkan bil Adama ta hanyar yanar gizo shi ma ya jawo hankalin mahalarta taron na kwanaki uku da ake gudanarwa, duk da cewa, kasar Sin ce ta gabatar da batun, amma yanzu ya samu karbuwa sosai daga daukacin al'ummun kasashen duniya, babban manajan kungiyar masu kula da adireshin yanar gizo ya gaya mana cewa, "A shekaru biyu da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar nan ta samar da kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama ta hanyar amfani da yanar gizo, ina ganin cewa, shawarar tana da ma'ana matuka, ni ma ina goyon bayanta sosai, yanzu haka muna hada kai tare domin cimma wannan buri."

Shugaban hukumar kare 'yancin mallakar fasahar masana'antu ta kasar Mexico Miguel Angel Margain ya yi nuni da cewa, babban taron intanet na kasashen duniya gagarumin biki ne a fannin yanar gizo a fadin duniya, ko shakka babu batutuwan da ake tattaunawa kan su yayin babban taron za su yi babban tasiri ga zaman takewar al'ummun kasashen duniya, ya ce, "Ina sa ran cewa, za a samu cikakkiyar nasara a wannan babban taron, abu mai faranta ran mutane shi ne kasar Sin ta kasance abin koyi a fannin raya tattalin arziki ta yanar gizo ga sauran kasashen duniya, a garin Wuzhen, na ga kusan dukkan matasa suna biyan kudi da wayar salula, ita ma kasarmu Mexico tana yin kwaskwarima a fannin sadarwa, muna iya koyon nasarorin da kasar Sin ta samu a wannan fannin."

Babban taron dake gudana a garin Wuzhen tsakanin ranar 3 zuwa 5 ga wata, ya hallara wakilai sama da 1500 daga kasashe da shiyyoyi fiye da 80.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China